Accessibility links

Jihar Bauchi Tayi Barazanar Korar Ma’aikatan Dake Gurguntar Da Aikin Rigakafin Shan Inna


Yarinya tana karban rigakafin cutar polio

Gwamnatin jihar Bauchi tayi barazanar korar duk ma’aikacin lafiyar da bai dauki yaki da cutar shan inna da aminci ba.

Gwamnatin jihar Bauchi tayi barazanar korar duk ma’aikacin lafiyar da bai dauki yaki da cutar shan inna da aminci ba.

Gwamna jihar Bauchi Isa Yuguda ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai. Gwamna Isa Yuguda yace gwamnatin jihar zata ci gaba da aikinta na yaki da cutar shan inna (PEI) da kuma ayyukan allurar rigakafi (EPI).

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin ta cinma nasarori sosai kan allurar rigakafi daga kashi 46% a shakara ta 2012 zuwa kashi 77% a watan shida na, 2013. Ya kuma ce gwamnatin zata kara kokari domin ganin an cimma nasarar shawo kan yaduwar kwayar ciwon shan inna baki daya.

Gwamnan Isa Yuguda yayi kira ga ‘yan jarida su kara bada bada labarin abinda ya shafi aikin da ake yi da kalubalar da ake fuskanta da kuma goyon bayan da ake bukata daga al’umma domin nasarar shirin yaki da kuma rigakafin maganin shan inna.

Gwamnan jihar, wanda mataimakinsa Alhaji Sagir Aminu Saleh ya wakilce shi, yace jihar zata sakawa ma’aikatan lafiya da suka yi aiki nagari.

Kungiyar kula da harkokin lafiya ta jihar ce ta shirya taron tare da hadin guiwar kungiyar ‘yan jarida ta jihar masu yaki da cutar shan inna.
XS
SM
MD
LG