Accessibility links

An Samu Cigaba Wajen Kawar da Yada Cutar Kanjamau Daga Uwa Zuwa ga Jariri


Uwa da jariri

An samu babban ci gaba wajen kare yada kwayar cutar HIV daga Uwa zuwa ga Jariri, kwayar cutar da a yanzu bata da wani takamammen magani wadda kuma take kawo cutar kanjamau inda aka iya tserar da fiye da jarirai 850,000 daga wannan cutar a tsakanin shekara ta 2005 da 2012, bisaga rahoton hukumar ta UNICEF.

An samu babban ci gaba wajen kare yada kwayar cutar HIV daga Uwa zuwa ga Jariri, kwayar cutar da a yanzu bata da wani takamammen magani wadda kuma take kawo cutar kanjamau inda aka iya tserar da fiye da jarirai 850,000 daga wannan cutar a tsakanin shekara ta 2005 da 2012, bisaga rahoton hukumar ta UNICEF.

A cikin wani sabon rahoton na 2013 da aka fitas wanda yake magana akan yara a kanjamau, rahoton ya nuna cewa a shekarar da ta wuce, yara 260,000 ne suka kamu da cutar idan an kwatanta da 540,000 a 2005.

"Wannan ruhoton yana tuna mana da cewa “zamani mara cutar kanjamau” shine wanda ake haihuwar dukan jarirai ba tare da wannan cutar ba, kuma su kasance haka – daga haihuwa zuwa iyakacin rayuwarsu – kuma yana nufin samar da magani ga dukan yara dake rayuwa da kanjamau,” inji Michel Sidibe, directa na kungiyar kare cutar kanjamau ta Majalisar Dinkin Duniya.

Ya ci gaba da cewa "Hakanan kuma ta tuna mana cewa ya kamata lafiyar mata da kuma kasancewarsu lafiya ya zama wani babban aikin kungiyar kiyaye kanjamau. Bani da shakkar zamu ci nasarar wannan manufofin.”

Godiya ga sabon maganin kiyaye cutar kanjamau (wanda ake kira Option B+), akwai babbar damar tallafawa mata masu rayuwa da kanjamau da kuma kiyaye yaduwar kwayar ga jarirai lokacin ciki, haihuwa da kuma yayin shayar da mama. Wannan maganin ya hada da shan kwayar magani daya a kowace rana.

"A cikin kwanakin nan da muke ciki, ko da mace mai ciki na dauke da cutar, baya nufin cewa dole dan ta ya sami wannan cutar ba shima, kuma yana nufin cewa kasancewa da wannan kwayar cutar ba zai hana matar ta yi rayuwa mai nagari ba,” inji Daraktan Asusun Tallafawa Yara, Anthony Lake.

Bisa kiyascewar Majalisar Dinkin Duniya, yawancin nasarorin da aka cinma an same su ne a kasashen da suka fi fama da nawayar cutas na Afrika.
XS
SM
MD
LG