Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar China ta Bada Maganin Zazzabin Cizon Sauro Ga Kasar Chadi


Sauro da yake kawo ciwon zazzabi

Ambasadan China a kasar Chadi Hu Zhiqiang ya mika magungunan zazzabin cizon sauro wadanda kudadensu ya kai fiye da kimanin miliyan 680,000 na dalar Amurka ga kamfanin magani na kasar Chadi.

Ambasadan China a kasar Chadi Hu Zhiqiang ya mika magungunan zazzabin cizon sauro wadanda kudadensu ya kai fiye da kimanin miliyan 680,000 na dalar Amurka ga kamfanin magani na kasar Chadi.

Hu yace, "Wannan ya nuna mahimmancin da shugabannin kasashenmu biyu suka bayar ga maganar lafiya. Ina fata wannan hadin kan tsakanin kasashen zai cigaba.”

Yayinda yake karbar magungunan, ministan lafiya na kasar Chadi Mahamat Annou Wadak yayi godiya ga kasar China domin wannan taimakon, kuma ya nuna cewa wannan yana cikin shirin gwamnatin Chadi na yaki da zazzabin cizon sauro.

Ya yiwa Ambasadan China alkawarin cewa wannan maganin zai kai ga mutanen da ke bukatar sa.

Wadak yace taimakon maganin na China, wanda shine kashi na biyu cikin wannan shekarar, yazo ne a daidai lokacin da ake samun karuwar mutanen da ke fama da zazzabinccizon sauro a kasar Chadi.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG