Accessibility links

Rahotanni daga Kano sun ce an samu barkewar cutar kwalara har ma an kwantar da mutane fiye da dari a asibiti.

Barkewar cutar kwalara cikin birnin Kano ta sa wasu sun ruga zuwa asibitin zana da 'yayansu domin karbar magani.

Kawo yanzu fiye da mutane dari ke kwance a asibiti sanadiyar wanna cutar kwalara mai haddasa amai da gudawa. Bullar cutar a wasu sassan birnin na Kano ya soma faruwa ne tun kimanin makwanni uku da suka wuce.

Amma wani darakta a ma'aikatar kiwon lafiya ta jihar Kano Dr. Tijani Husseini ya ce sun fara ganin karuwar amai da gudawa kusan sati hudu da suka wuce. Kuma duk wanda aka kawo asibiti da cutar ana bashi magani kana a bishi zuwa inda yake zaune a tsaftace nuhallin da magani domin hana yaduwar cutar. Ma'aikatan kiwon lafiya sun bi duk gidajen da mutane suka fito daga ciki da cutar.

Saidai ga bisa alamu kamar matakan basa tasiri idan aka yi la'akari da cigaba da karuwar mutane dake kamuwa da cutar wadanda galibinsu suna kwance ne a kasa ba tare da sun sami gadon kwanciya ba. Dr Husseini ya ce asibitin zana nada gadajen kwalara 70 ne. Gadajen kwalara daban ake yinsu wadanda suke asibitin yanzu sun fi 70. Dole ne wasu su kwanta a kasa domin ba za'a kwantar da mai ciwon kwalara ba a wani gadon da ba na kwalara ba ne. Ya ce cutar kwalara cuta ce wadda cikin awa daya ko biyu idan ba'a daba kulawa ba mutum zai galabaita har ma ya mutu. Don haka maimakon a mayar da mutum gida domin babu gadon kwalara sai a yi masa tanadi a kasa a bashi kulawar da yake bukata ya yarke. Idan an tura mutum gida domin rashin gado yana iya rasa ransa.

Dr Husseini ya yi bayani kan abun dake da nasaba da karuwar cutar. Ya ce wasu da suka kawo wanda ya kamu da cutar sai su zauna suna tare da wanda ya kamu bisa ga al'ada amma daga baya shi ma sai ya kamu. Sabili da haka ya ce sun tanadi wasu cibiyoyi na musamman domin kula da masu kwalara.

Dr Tijani Husseini ya shawarci jama'a su tabbata sun tsaftace ruwan da suke sha. Idan basu da kilorin suna iya dafa ruwan kafin su sha. Idan mutum ya shiga bandaki ya tabbatar ya wanke hannunsa da sabulu ko da toka. Mutum ya guji cin abincin da ba'a dafa ba. Idan mutum ya sayi kamar zobo a hanya to ya yi hankali. Idan kuma an sayi kayan marmari ya tabbatar ya wankeshi. Yakamata mutane su tsaftace muhallinsu da bandakinsu su kuma gujewa kazanta.

Ga karin bayani.

XS
SM
MD
LG