Kyanda, kwayar cutar ce mai saurin yaduwa ta iska a duk lokacin da mai cutar ya yi numfashi, atishawa ko tari.
Ana iya kare kamuwa da ita ta hanyar allurar rigakafi kuma an yi amannar an kawar da cutar daga Amurka tun 2000.
Jami’an kiwon lafiya na jihar Texas sun fada a ranar Talata cewa an samu sabbin mutum 25 da suka kamu da cutar kyanda tun karshen makon da ya gabata, wanda ya kawo jimlar wadanda suka kamu a Texas zuwa 223. Mutane 29 a Texas na kwance a asibiti.
Jami’an kiwon lafiya na New Mexico sun sanar da sabbin wadanda suka kamu uku a ranar Talata, wanda ya kawo jimillar wadanda suka kamu a jihar zuwa 33.
Barkewar cutar ta bazu daga Gundumar Lea, wacce ke makwabtaka da al’ummomin Yammacin Texas a cibiyar barkewar cutar, da ta hada da mutum daya da ya kamu a Gundumar Eddy.
Ma’aikatar lafiya ta jihar Oklahoma ta ba da rahoton wasu mutum biyu da ake kyautata zaton kyanda ce a ranar Talata, tana mai cewa suna da alaka da barkewar cutar a Yammacin Texas da New Mexico.
Wani yaro dan makaranta ya mutu sakamakon cutar kyanda a Texas a watan da ya wuce, kuma New Mexico ta ba da rahoton mutuwa ta farko da ke da alaka da cutar kyanda a cikin makon da gabata.
An ba da rahoton bullar cutar kyanda a jihohin Alaska, California, Georgia, Kentucky, Maryland, New Jersey, New York, Pennsylvania da kuma Rhode Island.
Dandalin Mu Tattauna