Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Kyanda Ta Kashe Yara 80 A Zimbabwe


Yiwa yara allaurar rigakafin Kyanda a lardin Manicaland (Twitter - @WHO_Zimbabwe)
Yiwa yara allaurar rigakafin Kyanda a lardin Manicaland (Twitter - @WHO_Zimbabwe)

Ma’aikatar lafiya ta ce barkewar cutar Kyanda ta kashe yara 80 a kasar Zimbabwe tun daga watan Afrilu, inda ta dora alhakin kan tarukan da coci-coci ke yi.

A cikin wata sanarwa da kafanin dillanci labarai na Reuters ya gani a ranar Lahadi, ma’aikatar ta ce barkewar cutar yanzu ta bazu a duk fadin kasar, inda adadin wadanda suka mutu ya kai kashi 6.9 cikin 100.

Sakataran Lafiya, Jasper Chimedza, ya ce ya zuwa ranar Alhamis, an samu rahoton mutane dubu 1,036 da ake zargin sun kamu da cutar, yayin da 125 aka tabbatar sun kamu da cutar tun bayan barkewarta, inda a yankin Manicaland da ke gabashin Zimbabwe ke da mafi yawan wadanda suka kamu da cutar.

Chimedza ya fada a cikin sanarwar cewa “Ma’aikatar lafiya da kula da yara na son sanar da jama’a cewa barkewar annobar kyanda da aka fara bada rahoto a ranar 10 ga watan Afrilu da ya gabata, ta yadu a fadin aksar tun lokacin bayan tarukan coci.”

“Wadannan tarukan da suka samu halartar mutane daga larduna daban-daban na kasar da ba’a san ko sun yi allurar rigakafin cutar ba lamarin da ya haifar da yaduwar cutar kyanda zuwa wuraren da ba’a taba samun bullar cutar ba.

Manicalanda, lardi na biyu mafi yawan jama’a, yana da wadanda suka kamu 356 da kuma wadanda suka mutu 45, in ji Chimedza.

Ya kara da cewa, galibi wadanda suka kamu da cutar na cikin yara yan tsakanin watanni shida zuwa 15 daga kungiyoyin addini, wadanda ba’a yi musu allurar rigakafin cutar kyanda ba saboda dalilai na addini.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG