Accessibility links

Da misalin karfe uku da minti arba'in da biyar aka samu tashin wasu bamabamai a wasu wurare a Maiduguri

Tashin bamabaman sun yi sanadiyar wasu mutane da dama da kuma jikata wasu.

Bam din farko ya tashi ne a cikin tashar Baga cikin Maiduguri. A nan ya hallaka mutane da dama da kuma wasu dake hada-hada a lokacin. Rahotanni sun ce wasu 'yan kunar bakin wake ne mata suka tada bam din.

A wani wurin kuma an ajiye bam kusa da inda mutane ke yin salla amma ba'a cikin masallaci ba.

Akwai wani bam kuma da ya tashi amma ya hallaka 'yar kunar bakin waken ne kawai a wani wuri da ake kira Biyok akan titin Baga. 'Yar kunar bakin waken ce ta tarwatsa kanta da kanta kafin ta isa wurin jama'a.

Da zara an samu karin bayani zamu kawo maku. Yanzu ga rahoton Haruna Dauda Biu.

XS
SM
MD
LG