Accessibility links

Taron Hafsan Hafsoshin Kasashen Gabar Tafkin Chadi


Air Marshal Alex Badeh Hafsan Hafsoshin Najeriya

An bude taron hafsan hafsoshin kasashen dake gabar tafkin Chadi, wato Najeriya, Nijar Kamaru, Chadi har da Benin a babban birnin Najeriya Abuja.

Da yake jawabi a taron hafsan hafsoshin kasashen gabar tafkin Chadi Air Marshal Alex Badeh na Najeriya yace kalubalen ta'adanci ya shafi duk kasashen dake yankin da ma duniya gaba daya. Saboda haka, taron, yace yana da mahimmanci.

Taron zai duba hanyoyin da zasu hada gwiwa domin su yaki Boko Haram da kowace kungiyar ta'adancin a yakinsu da kuma tabbatar da doka da oda.

Alex Badeh yace babu mugun ta'adanci da ya rike masu wuya irin ta'adancin Boko Haram wanda ya jefa al'umma cikin mawuyacin hali da karya tattalin arziki..

Badeh ya cigaba dacewa su 'yan ta'ada babu ruwansu da iyakar kasa da kasa. Koina kutsawa suke yi. Saboda haka ya zama wajibi kasashen su hada karfi da karfe su magance matsalar.

Babban daraktan tafkin Chadi Sanusi Imrana yace taron zai ba sauran kasashen duniya damar tallafawa kasashen tafkin Chadin wajen kawo tsaro da farfado da tattalin arziki.

Masana harkokin tsaron Najeriya irinsu Rabe Nasir na mara baya wa irin wannan gamayyar da nanata matukar aka sakarwa sojoji mara da tsame son zuciya za'a iya cimma nasarar yakin.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

XS
SM
MD
LG