Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sassauta Dokar Hana Fita A Jos da Bassa


Gwamnan Filato Simon Lalong (Facebook/PLSG)
Gwamnan Filato Simon Lalong (Facebook/PLSG)

Gwamna Simon Lalong na jihar filato ya sassauta dokar hana fita da ya saka a wasu sassa na jihar kamar garin Jos da Bassa sakamakon rikicin da ya barke a jihar da ya haifar da rashin tsaro.

A wani jawabi da ya yi wa jama'ar jihar Filato a yau Litinin, gwamnan jihar Simon Lalong ya ce yanzu dokar hana fita ta sa'o'i 24 da gwamnati ta sa a Jos ta Arewa za ta koma daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe.

Wannan ne karo na 2 da ake sassauta dokar wadda ta kasance sa'o'i 24 da farko, domin a 'yan kwanan baya ma an dan sassauta dokar ta koma daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe.

Lalong ya kuma ce har yanzu dokar haramta zirga-zirgar a daidaita sahu, wato keke Napep da masu talla tana nan da a cikin garin Jos da Bukuru.

Har ila yau, gwamna Lalong ya sanar da cewa an dage babban taron tattalin arziki da saka hannun jari na jihar Filato da aka shirya yi ranar 1 da 2 ga watan Satumba, inda ya ce gwamnati za ta sanar da sabuwar ranar da za'a gudanar da taron.

Hare-haren baya-bayan nan a kananan hukumomin Jos ta Arewa, Bassa, Riyom, da ma Barikin Ladi ya sanya al’umma mazaunan jihar Filato cikin yanayin zaman dar-dar.

Kimanin mutane 36 ne aka kashe a kauyen Yelwa Zangam dake gundumar Zangam na karamar hukumar Jos ta arewa a jihar ta Filato a makon jiya kadai.

Lamarin ya kai ga wasu gwamnonin jihohi suka aika tawagar kwashe dalibai yan asalin jihar su da ke karatu a jami’ar gwamnati na jihar Filato don gujewa abin da kan je ya dawo bayan da tuni aka rufe jami’ar.

A yayin da wasu ke danganta kashe-kashen da rikicin kabilanci da na addini, gwamnatin jihar ta ci gaba da cewa kashe-kashen aiki ne na wasu batagari masu aikata muggan laifuffuka ne kawai wanda dole ne a hukunta su.

Wasu kuma na alakanta rikicin da kisan gilla da aka yiwa wasu matafiya Fulani da ke kan hanyarsu ta komawa jihohin da su ke zaune bayan halartar wa’azin zagayowar sabuwar shekarar musulunci a masalacin Dahiru Bauchi a jihar Bauchi.

An wayi garin ranar 15 ga watan Agusta da labarin yadda wasu batagari suka yiwa fulani matafiya sama da 27 kisan gilla a unguwar Gada-Biyu dake kan hanyar Rukuba na jihar Filato.

Gwamna Lalong ya bayyana cewa yana kan aikin tuntuba da hulda da manyan masu ruwa da tsaki wadanda suka hada da sarakunan gargajiya, shugabannin siyasa, sauran al'umma da shugabannin addini don neman mafita mai dorewa ga matsalar tsaro da ke cigaba da addabar jihar Filato.

Gwamnatin jihar Filato ta kuma tsaurara matakan tsaro a majalisar jihar da sauran wurare.

XS
SM
MD
LG