Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Sabon Hari A Jihar Filato Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane Akalla 35


'Yan Bindiga

‘Yan ta’adda sun kai wani sabon farmaki a garin Jos ta jihar Filato, inda suka yi harbi tare da cinnawa gidajen mutane wuta, lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 35.

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun kai hari ne a daren Talata kan al’ummar Yelwa Sangam da ke karamar hukumar mulkin Jos ta Arewa, a jihar Filato da ke Arewacin Najeriya.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa ko baya ga harbe mutane da dama, ‘yan ta’addar sun kuma kona wasu iyalai da ransu a cikin gidajensu.

Wasu majiyoyi sun ce maharan sun karya gadar da ke zuwa yankin kafin su kai farmakin, domin hana kai wa al’ummar dauki a lokacin da suke gudanar da karen aikin na su.

'Yan bindiga sun kona gidaje a Jos
'Yan bindiga sun kona gidaje a Jos

Al’ummar ta Yelwa dai tana makwabtaka da gidajen daliban jami’ar Jos, to sai dai babu rahoton dalibi ko daya da lamarin ya shafa.

Du da haka an gaggauta kwashe daliban jim kadan bayan aukuwar harin, a yayin da kuma wasu iyaye da dama suka je domin dauke yaransu, bayan da hukumomin jami’ar suka ba da sanarwar rufe karatu na dan wani lokaci.

Harin ya auku ne a daidai lokacin dokar hana fita da gwamnatin jihar ta kakaba daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe, sakamakon harin da wasu ‘yan gari suka kai wa wasu matafiya a makon da ya gabata, kuma yankin na Jos ta Arewa na daga cikin wuraren da lamarin ya shafa.

Wannan harin kuma na zuwa ne ‘yan sa’o’i bayan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da gwamnan jihar ta Filato Simon Lalong, dangane da hare-haren da ake kai wa da ke sanadiyyar rasa rayuka a jihar ta Filato.

XS
SM
MD
LG