Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An shawarci fadar shugaban kasar Najeriya kan matakan cimma muradun karni


Wata mata da yan yaran ta
Wata mata da yan yaran ta

An yi kira ga gwamnatin tarayyar Najeriya ta bada fifiko kan kula da samar da abinci mai gina jiki ga mata masu juna biyu da kanannan yara

An yi kira ga gwamnatin tarayyar Najeriya ta bada fifiko kan kulawa da samar da abinci mai gina jiki ga mata masu juna biyu da kanannan yara, a tsarin gwamnatin na inganta tattalin arziki da jin dadin rayuwar al’umma, ta wajen kafa ma’aikatar abinci da sinadirai masu gina jiki ko kuma ma’aikatar lafiya da abinci mai gina jiki.

An bada wannan shawarar ne bayan wani taron kwana uku kan ciyar da kasa da abinci mai gina jiki da aka gudanar da nufin daukar matakan cimma muradun karni. Mahalarta taron da suka hada da kwararru a fannin kiwon lafiya da kungiyoyi masu zaman kansu dake kula da lafiyar mata masu juna biyu, da kananan yara, da jami’an jami’a da kungiyiyin addinai da na al’umma sun bayyana rashin gamsuwa da halin da mata da kananan yara suke ciki.

Taron ya kuma shawarci karamin ministan lafiya Dr Mohammed Pate ya kafa kwamitin da zai gabatar da wannan bukatar a fadar shugaban kasa da majalisar dokoki ta kasa da shugabannin al’umma da na kungiyoyin addinai.

Bisa ga cewar taron, ana bukatar hadin kai da goyon bayan al’umma da kuma mika wuya a fannin gwamnati domin nasarar cimma muradun karni.

Mahalarta taron sun ce zai yi wuya Najeriya ta iya cimma gurorinta na lafiya da ilimi da tattalin arziki dake tsarin muradun karnin ba tare da aiwatar da shirye shiryen samar da abinci masu gina jiki ba.

Suka kuma bada shawarar samun kwararre da ya kai mukamin darekta da zai yi aiki a kwamitin kula da harkokin abinci da kuma sinadaran gina jiki karkashin hukumar tsare tsare ta kasa. A kuma samar da kudi musamman domin gudanar da wannan aikin.

XS
SM
MD
LG