Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu ilimin kimiyya a Najeriya sun bayyana illar Fansidar a jinyar mata masu juna biyu


Ana gwajin maganin cutar cizon sauro

Masu ilimin kimiyya a Najeriya sun ce amfani da maganin Fansidar yana kara yada kwayar cutar maleriya a tsakanin al’umma

Masu ilimin kimiyya a Najeriya sun hakikanta cewa amfani da maganin Sulphadozine-Pyrimethamnin da aka fi sani da Fansidar wajen jinyar mata masu juna biyu ba tare da la’akari da amfani da gidan sauro da aka jika da magani da suke yi ba, yana kara yada kwayar cutar maleriya a tsakanin al’umma.

Kwararrun da suka gudanar da bincike tsakanin mata masu juna biyu 306 dake zuwa awo a wani asibitin gwamnati dake birnin Ibadan , sun gano cewa, amfani da maganin Fansidar kadai wajen jinyar mata masu juna biyun dake fama da zazzabin cizon sauro, yana sa kwayoyin cutar dake haddasa zazzabin cizon sauro su sami maboya a jininsu musamman a yankunan da cutar ta zama annoba a duniya.

Hukumar lafiya ta duniya ta shawarci dukan kasashe su nemi hanyar hana mata masu ciki kamuwa da zazzabin cizon sauro domin shawo kan illar da cutar ke haifarwa tsakanin mata masu juna biyu.

Masu binciken sun bayyana damuwa ganin cewa, kasa da kashi daya bisa ukun matan da aka gudanar da binciken a kansu suke iya samun gidan sauro da aka jika a magani.

Rahoton da aka buga a mujalla aikin jinya ta shekara ta 2012 ya yi nuni da cewa, idan har zurfin bincike ya tabbatar da wannan lamarin, duk da yake amfani da maganin Fansidar yana taimakawa a jinyar masu gama da zazzabin cizon sauro, yana yiwuwa ya kara hadarin yaduwar cutar da zai zama daga baya kwalliya bata biya kudin sabulu ba.

Kwararrun sun bada shawarar kara maida hankali wajen samar da gidan sauron da aka jika a magani musamman ga mata masu juna biyu da kananan yara idan ana so a cimma burin muradun karni.

XS
SM
MD
LG