Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Shawarci Trump a Kan Abubuwan da Zai yi a Ziyararsa a Korea ta Kudu


Shugaba Trump

Wasu ‘yan kasar Korea ta Arewa guda hudu da suka arce daga kasar su sun shaidawa Muryar Amurka a wasu sakonni bidiyo abubuwan da suke son shugaban Amurka Donald Trump ya yi da kuma abubuwan da suke ganin yakamata ya fada a ziyarar da zai kai Korea ta Kudu.

An gabatar da sakonnin ne kafin shugaba Trump ya tashi zuwa Korea ta Kudu da safiyar yau Juma’a a wata ziyarar kwanaki 12 zuwa kasashe biyar wanda ake ganin zai maida hankali a kan barazanar kera makaman nukiliya da Korea ta Arewa keyi da makamai masu lizzami. Shugaba Trump zai gana da shugaban Korea ta Kudu Moon Jae-in a birnin Seoul a ranar bakwai ga wannan watan Nuwamba.


Ana sa ran batutuwar da suka shafi Korea ta Arewa ne zasu dauke hankali a wannan ziyara dake zuwa lokacin da Amurkawa suke bayyana ra’ayi cewar Korea ta Arewa ce babban barazanar da Amurka ke huskanta a cikin wannan lokaci.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG