Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Soma Amfani Da Riga Kafin Cutar Ebola A Kasar Congo


 Ma'aikacin jinya a Goma, Jmhuriyar Dimokaradiyar Congo
Ma'aikacin jinya a Goma, Jmhuriyar Dimokaradiyar Congo

Hukumar zartarwar kungiyar Tarayyar Turai a wannan mako ta bada izinin sarrafa rigakafin cutar Ebola

Tuni da hukumar lafiya ta duniya (WHO), ta bayyana wannan a matsayin gagarumar nasara ga kiwon lafiyar duniya, wanda kuma wannan zai iya canja al’amura a yaki da ake yi da cutar.
Wannan ne karon farko da aka amince da yin amfani da maganin Ebola a ko ina a duniya.

Mai Magana da yawun WHO Christian Lindmeier ya fadawa Muryar Amurka cewa wannan mataki ne mai muhimmanci kuma gagarumar nasara ce ga kiwon lafiyar al'umma.

Wannan zai gaggauta shirin shiga da maganin a cikin kasashe domin basu lasisin da zasu iya yin magani da kuma samar da adadi mai yawa a duk inda ake bukatar magani ko kuma inda ake gani za a iya samun barkewar cutar domin baiwa ma’aikatan da masu bada gudunmuwa dama su kimtsa a yakin da cutar ta Ebola.

Maganin da yake matakin gwaji, ana ci gaba da amfani da shi a wuraren da aka samu barkewar cutar Ebola a gabashin Demokaradiyar Jamhuriyar Congo. An yi amfani dashi aka kare sama da mutane dubu 250 a lardunan Ituri da Kivu ta Arewa na kasar DR Congo.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG