Accessibility links

An Soma Musayar Kalamu Kan Murabus Da Bamanga Tukur Ya Yi.


Alhaji Bamanga Tukur shugaban PDP mai murabus
A wani lamarin da ba'a yi zato ba shugaban jam'iyyar PDP wadda ta shiga wasu rigingimun siyasa ya yi murabus kwana daya bayan wasu sun sha alwashin ba zai bar kujerarsa ba ko dama sama da kasa zasu hade.

Tuni a jihar Adamawa jihar Bamanga Tukur mutane suka fara mayar da kalamu game da labarin cewa ya yi murabus daga mukaminsa. Yayin da 'yan adawa ke nuna farin cikinsu su kwa 'yan bangaren Bamanga Tukur cewa suke ba haka lamarin ya ke ba. Mr. Peter Ilesha sakataren PDP bangaren Kugama dake jayayya da PDP bangaren Bamanga Tukur cewa ya yi Allah ya raka taki gona. Amma kuma ya ce kodayake suna murna a wani gefen kuma suna yaba masa da daukan wanann matakin domin tsarin mulkin PDP ya ce koda majalisar zartaswar jam'iyyar ta tsige mutum sai an je babban taron jam'iyyar kafin a tabbatar da hakan. Amma murabus da ya yi ya kawo masa abun da sauki. Ya ce yanzu PDP zata samu ta cigaba. Ya ce dama rikicin jam'iyyar a jihar Adamawa ya fara kafin ya yadu kuma sun fada tun farko idan ba'a yi gyara ba jam'iyyar zata sha wuya.

'Yan bangaren Bamangan irin su Barrister A. T. Shehu kuma sakataren jam'iyyar bangaren Bamanga ya musanta batun cewa shugaban jam'iyyar ya sauka daga mukaminsa. Ya ce har karfe taran daren jiya Bamanga ne shugaban PDP a Najeriya. Idan har daga baya ya mika takardar yin murabus ba abun mamaki ba ne domin sau da yawa ya so ya bari mutane ne suka matsa masa ya cigaba.

An zuba ido a ga yadda zata kaya yayin da sanatoci goma sha bakwai daga PDP ke shirin canza sheka zuwa APC. Sanato Umaru Jibirila shi ya sanarda niyar komawa APC da zara majalisar dattawan ta koma bakin aiki. Ya ce zalunci da rashin gaskiya da shugabanninsu ke nunawa sun yi yawa.

Ga karin bayani.

XS
SM
MD
LG