Accessibility links

Wai Shugaban Kasa Bai Ce Bamanga Ya Yi Murabus Ba


Alhaji Bamanga Tukur, shugaban PDP

Yau a ke zaton manyan PDP zasu yi taro inda ana zaton shugaban jam'iyyar Alhaji Bamanga Tukur zai rasa kujerarsa to amma Gulak mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa ya ce ba haka ba ne.

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa ya ce ba gaskiya ba ne wai shugaban kasa ya umarci Alhaji Bamanga Tukur ya yi murabus.

Ta bakin Gulak ya ce duk maganganun jaridu ne. Babu randa shugaban kasa Goodluck Jonathan ya gayawa Alhaji Bamanga Tukur ya yi murabus ko kuma za'a saukar da shi a taronsu na yau. Idan ma za'a cewa Bamanga Tukur ya yi murabus akwai matakai da za'a bi.Ya ce wannan dabarun 'yan jam'iyyar adawa ne da sukE shigarwa cikin jam'iyyar PDP suna kuma yin aanfani da jaridu kalakala su nuna kamar akwai wata matsala a cikin PDP da ba za'a iya yin maganinta ba. Iyayen jam'iyyar PDP suna tsaye daram kuma zasu shawo duk wata matsala da ta addabi jam'iyyar.

Kan ko sun gamsu da yadda Alhaji Bamanga Tukur ke jan akalar PDP Gulak ya ce ba kowa da kowa ba ne zai ce ya gamsu da shi ba.Ya ce akwai wadanda su ke da banbancin ra'ayi. Ya ce jam'iyya ce ta kowa da kowa kuma sai an tattauna a san yadda za'a shawo kan matsalolin.

To sai dai Barrister Gulak ya ki ya tabbatar ko a taron da aka yi jiya da gaske ne Alhaji Bamanga Tukur ya ki sauka wai sai an je babban taron jam'iyyar. Amma a taron yau ya ce ya danganta da abun da manya manyar ja,'iyyar zasu tsayar kuma duk abun da ya faru 'yan jarida zasu samu labari.

Ga karin bayani.

XS
SM
MD
LG