Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tsaurara Matakan Tsaro a Yankin Matatar Man Kamaru


Hukumomi a kasar Kamaru sun kara tsaurara matakan tsaro a yankin matatar man kasar, biyo bayan wata fashewar bututun mai da ya faru a karshen mako, wanda yayi sanadiyar rufe matatar.

Hukumomin sun musanta cewar mayakan sa kaine suka kai harin, sun kuma kara da cewar baza’a samu karancin mai ba a sanadiyyar rashin aikin matata.

Fashewar tayi sanadiyar tashin gobara da tayi sanadiyyar lalacewar wasu na’urori, amma ba’a rasa rai ba.

Ministan kasuwanci na kasar Kamaru Luc Magloire Mbarga Atangan ya tabbatar da cewar ba za’a samu karancin mai ba ballantana Karin kudin sa.

Ya ce shekaru 2 da suka gabata Kasar ta taba samun kanta a cikin irin wanna halin, lokacin da aka rufe matatar har na tsawon watannin 8 don aiwatar da wasu gyare-gyare, kuma karanci Mai da aka samu bai yi wani tasiri ba. Domin kuwa sun kara yawan Man da ake shigowa da shi ba tare da kara kudin Man ba. Ya bukaci jama’a da su kwantar da hankalinsu kada su tsorata.

Facebook Forum

Zauren VOA Hausa #EndSARS

Zauren VOA Hausa #EndSARS Kashi na Biyu 03
please wait

No media source currently available

0:00 0:18:31 0:00
Karin bayani akan #ENDSARS: Zanga Zangar Kyamar Gallazawa Al’umma Da Yan Sanda Ke Yi

Zauren VOA daga jihar Kaduna Alan Almajiranci da Cin Zarafin Mata - 3

Zauren VOA daga jihar Kaduna Alan Almajiranci da Cin Zarafin Mata - 3-1
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:55 0:00

Rayuwar Birni

Rayuwar Birni: Hira da Aliyu Danlami mai sayar da furanni a Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:49 0:00
XS
SM
MD
LG