Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tsige Kunle Oluomo Daga Shugabancin Majalisar Dokokin Jihar Ogun


Oluomo
Oluomo

Majalisar Dokokin Jihar Ogun ta tsige Shugabanta, Kunle Oluomo, daga kan mukaminsa.

Sha takwas (18) daga cikin mambobin majalisar 26 suka kada kuri’ar tsige Mr. Oluomo a yayin zamanta na ranar Talata.

An tsige Mr. Oluomo ne a bisa zarginsa da wawure kudade da rashin jin shawara da wasu laifuffukan masu nasaba da wadannan.

Nan take Majalisar ta zabi wani mamba mai suna, Oludaisisi Elemide, ya maye gurbinsa a matsayin sabon shugaba.

A jawabinsa na farko tun bayan dambarwar tsigewar, sabon Shugaban majalisar ya bukaci samun kwanciyar hankali tsakanin mambobinta.

Ya kara da cewar, sabanin yadda wasu ke rade-radi, ba’a tsige tsohon shugaban majalisar ne domin yakar gwamnan jihar Dapo Abiodun ba.

Ya ci gaba da cewar, al’amarin na cikin damar da Kundin Tsarin Mulki Kasa ya baiwa ‘yan majalisar na zaben wanda suke so ya jagorancesu.

Daga bisani majalisar ta dage zamanta tsawon makonni 2, inda sandar girman majalisar ta kasance a hannun sabon Shugaban a matsayin wata alama ta jagoranci.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG