Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Neja Sun Ceto 4 Daga Cikin 17 Da ‘Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su


'Yan sanda Najeriya yayin wani atisaye da suka yi a Abuja (Hoto: Facebook/Rundunar 'Yan sandan Najeriya - Wannan tsohon hoto ne)
'Yan sanda Najeriya yayin wani atisaye da suka yi a Abuja (Hoto: Facebook/Rundunar 'Yan sandan Najeriya - Wannan tsohon hoto ne)

Rundunar ‘Yan Sandan jihar Neja ta tabbatar da ceto hudu daga cikin mutane 17 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su daga dajin Kpakuru da ke garin Kagarko a jihar Kaduna da kuma kauyen Chachi na karamar hukumar Tafa.

Idan ba a manta ba a baya an fitar da rahoton cewa ‘yan bindiga a wasu hare-hare guda biyu a ranar Talata, sun yi garkuwa da mutane 17 daga garin Garam da kuma al’ummar Zhibi duk a karamar hukumar Tafa ta jihar Neja.

A cewar wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar DSP Wasiu Abiodun ya sanya wa hannu, Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar Neja Shawulu Danmamman, a ranar 17/01/2024 ya aike da wata tawagar musamman karkashin jagorancin kwamandan yankin Suleja, ACP Sani Musa da ACP Muazu Muhammad, tare da Sashin Yaki da Masu Garkuwa da Mutane, Kungiyar Bada Agajin Dabara (TST), da kuma tawagar yan sintiri na yankin Suleja zuwa yankunan da suka kai ga ceto.

Kwamishinan ya kuma umurci tawagar da su fara sintiri na tabbatar da aminci da aikin sa ido a yankin domin dakile sake afkuwar lamarin tare da kara kaimi wajen ceto wadanda aka sace a hannunsu.

Garin Garam, inda aka yi garkuwa da mutane 14, yana kan hanyar Sabon-Wuse-Bwari, yayin da Zhib, inda kuma aka yi garkuwa da wasu mutane uku, wani yanki ne na al'umma da ke da iyaka da Dei-Dei, wanda ke karkashin karamar hukumar Bwari ta babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja.

~Yusuf Aminu Yusuf ~

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG