Alkalin wata babbar kotun kasar, ya tuhumi Fernandez da wasu tsoffin jami’ai a gwamnatinta, ciki har da Sakataren aikace-aikace, wanda aka tsare shi a watan Yuni, inda aka zarge shi da sace kudaden da aka ware domin shimfida hanyoyi.
Fernandez ta musanta hannu a wadannan zarge-zarge, inda ta dora laifin akan shugaban kasar na yanzu Mauricio Macri da sa hannu a harkokin shari’ar kasar domin a tuhume ta.
Har ila yau tsohuwar shugabar ta nemi da a yi bincike kan duk kudade kwantiragin da aka ware domin aikace-aikace a lokacin mulkinta.
Yanzu haka alkalin ya sa a rike wasu kudade da yawansu ya kai dala miliyan 633 a duk asusun wadanada ake zargi, koda babu tabbacin ko kadarorin su, sun kai darajar wadannan kudade.
Idan dai har aka samu toshuwar shugabar da laifi, akwai yuwuwar a yanke mata zaman gidan yari har na tsawon shekaru 10.