Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Bikin Yaye Jami'ai 583 A Makarantar Sojoji Da Ke Agadas a Jamhuriyar Nijar


Sojoji da aka yaye a Nijar

A wani mataki na kara yawan sojojin da Nijar ke da su an yi bikin yaye sojoji na kasashen Afurka masu magana da harshen faransanci bayan sun shafe watanni goma ana ba su horo kan dabarun yaki da ta'addanci inda Ministan Cikin Gida na Nijar ya jagoranci bikin.

Sama da jami'an tsaron 583 ne da suka fito daga kasashen Africa irinsu Kamaru, Mali, Ivory Coast, Congo Guinee dakuma jamhuriyar Africa ta tsakiya suka samu horon dubarun yaki na tsawan watanni goma (10) a makarantar horar da sojoji ta ENSOA dake Agadas.

Sojoji a Nijar
Sojoji a Nijar

Wannan horon na zuwa ne a daidai lokacin da jami'an tsaron kasar Nijar ke yaki da ta'addanci. Ministan Tsaron Kasar Nijar Alkasum Indatu shi ne ya jagoranci bikin. Ya ce wannan abun farin ciki ne na yaye da aka yi na jami'an kuma za mu rarraba su zuwa fagen daga. Ya kara da jan hanakli jami'an da suka sami horon da su dage wajen samar wa kasar ingataccen tsaro.

Sojoji a Nijar
Sojoji a Nijar

Masu sharhi kan al'Amurran tsaro na ganin wannan a matsayin hanyar da za a magance tsaro kuma ta kara adadin sojojin da kasar Nijar ke dasu da kuma basu wadatattun kayan aiki kamar yadda Ibrahim Manzo Jallo, mai sharhi kan al'amuran tsaro a Agadas ya bayyana.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:26 0:00

Shugaban Azman

Dalilin Da Yasa Muka Dakatar Da Tafiya Yajin Aikin Sufurin Jiragen Sama a Najeriya - Shugaban Azman
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:17 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sojojin Najeriya sun samu nasarar kwace bindigogi sama da 500

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Shugaban NDLEA a Najeriya, Janar Buba Marwa

Dalilin Da Ya Sa Muke Bin Diddigin Dukiyar DCP Abba Kyari - Buba Marwa
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:19 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Gwamna Matawalle

Dalilan Da Suka Sa Muka Sayi Motoci Ga Sarakuna A Zamfara - Gwamna Matawalle
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG