Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An yi Canjin-canzau a Harkar Siyasar Sokoto Inda Bafarawa ya Koma PDP


Tsohon Gwamnan Sokoto Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa

Dambarwar siyasar jihar Sokoto da ma ta Najeriya ta dauki wani sabon salo inda Alhaji Attahitu Bafarawa tsohon gwamnan jihar ya fice daga APC ya koma PDP

Siyasar jIhar Sokoto ta dauki wani salo daban inda tsohon gwamnan jihar Alhaji Attahiru Bafarawa a wani yunkuri na ba zata ya canza sheka daga APC zuwa PDP.

Tun shigar gwamnoni biyar daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar APC ita jam'iyyar APC ta shiga rigingimun siyasa a jihohi daban daban. A jihar Sokoto APC ta rabu gida biyu inda akwai bangaren gwamna Wamako da bangaren Bafarawa. Gwamna Aliyu Wamako da tsohon gwamnan jihar Alhaji Attahiru Bafarawa basa ga maciji tsakaninsu.

Wannan dambarwar tsakanin Wamako da Bafarawa ta sa bangaren Bafarawa ya fice daga APC jam'iyyar da Bafarawa na cikin wadanda suka kafata zuwa PDP, shi da magoya bayansa.

Alhaji Attahiru Bafarawa ya ce shiga PDP ba shawararsa ba ce. Magoya bayansa sun ce shigowar gwamna Wamako ta dagula masu lissafi domin idan gyara ake son a yi babu yadda za'a yi gyaran da gwamna Wamako. Tafiyarsu tare ba zata yiwu ba. Magoya bayansa suka ce ko shi Bafarawa ya tsaya cikin APC shi kadai su kuma su bar 'yam'iyyar. Ya ce ya tambayesu abun da suke so suka fada mashi suna son PDP. Ya ce shi baya siyasa domin a zabeshi. Yana yi ne domin abun da jama'arsa ke so. Sabili da haka sun sa shi cikin wani hali na kakanikayi. Ya ce yana da jama'a masu goyon bayansa ba a Sokoto ba kawai.

Alhaji Bafarawa ya ce mutanensa sun yanke hukunci kuma shi ya goyi bayansu zai bisu duk inda suke son su tafi. Sun zabi shiga PDP kuma shi ya bisu. Ya ce canji da suke son su kawo suna iya kawoshi a jam'iyyar PDP. Yanzu APC ta zama PDP domin irin abubuwan da ake gani a PDP su ne suke faruwa a APC. Sun shiga PDP su kawo canji. Ya ce kuma yana neman ahuwa daga magoya bayansa domin inda ya samu kansa yanzu. Ya yi alkawarin binsu ya yi masu bayani ya kuma rokesu su bishi zuwa PDP domin su kawo canji.

Dama can an sha zargin Bafarawa da yiwa jam'iyyar PDP aiki ta kawo rikici cikin jam'iyyar APC. Da aka tambayeshi kan wannan zargin sai ya ce batawa mutum suna ba a kansa aka fara ba. An yiwa Annabi Mohammed (S.W.A.) balantana shi. Ya ce idan a da shi bai zama dan kore ba babu abun da zai sa yanzu ya zama dan kore. Shi baya siyasa domin kowa sai domin jama'arsa. Ya ce ba'a iya sayensa da kudi ko mukami. Ya ce duk abun da ake nema Allah ya yi masa.

Wannan lamarin ka iya shafar sauran jihohi hudun da gwamnoninsu suka shiga APC domin tsohon gwamnan Kano Ibrahim Shekarau yana tattaunawa da Bafarawa domin su samu hanyar fita su da jama'arsu daga irin halin da suka samu kansu.
XS
SM
MD
LG