Accessibility links

A jihar Gombe APC tana zargin gwamnatin jihar da kama 'ya'yanta ba gaira ba dalili lamarin da tana gani wani yunkurin katura masu ne.

Jam'iyyar APC reshen jihar Gombe na zargin gwamnatin jihar da jami'an tsaro da hada baki suna kutuntawa 'yan jam'iyyar.

Shugaban kwamitin riko na jam'iyyar a jihar Gombe Barrister Magaji Dohol shi ya shaidawa Muryar Amurka lamarin da suka samu kansu a jihar Gombe. Ya ce sabili da PDP ta ga ba zata iya karawa da APC ba shi ya sa tana anfani da jam'an tsaro ta karya masu baya. Ya ce suna da labarin wadanda suke jagorantar irin abubuwan da ake yi masu. Ya ce wajen yaransu ashirin aka kama. Yaran ba yawo suke yi ba. Suna cikin ofishin jam'iyyar aka afka masu. Wasu kuma ana binsu gida-gida daga karfe biyun dare ana kamasu.

Ya kira 'yan jam'iyyarsu su fitar da tsoro daga zukatansu kuma kada su bari wani abu ya razanasu.

Amma ta bakin kakakin 'yansandan jihar Gombe DSP Attajiri zargin na APC ba kashin gaskiya ciki. Ya ce su 'yansanda babu ruwansu da wata jam'iyya. Wadanda suka kama mutane ne rike da makamai zasu je su yi abun da bai kamata ba. Su ne suka kama. Ya ce sun kama mutane da adduna da bindigogi da wasu makamai. Ya ce wadanda suka kama lokacin da suke sintiri 'yan bata gari ne. Kuma tuni sun gurfanar da su a kotu. Ya ce sun tara 'yansiyasa sun gargadesu da su yi siyasa bisa ga abin da doka ta tanada. Duk wadanda ba zasu bi doka ba hakinsu ne su kama su domin su kare jama'a.

Junaidu Usman Abubakar shi ne mai tallafawa gwamnan jihar Gombe ta fannin jaridu ya ce zargin na APC babu gaskiya ciki. Ya ce harka ce ta dan adawa wanda komi ya faru sai ya juya magana domin ya shafawa wani kashin kaji. Ya ce kowa ya san akidar gwamnan jihar Gombe. Siyasarsa bata tada hankali ba ce. Yana yin siyasa cikin kwanciyar hankali da kuma natsuwa.

XS
SM
MD
LG