Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Jana’izar Gomman Mutanen Da 'Yan Bindiga Suka Kashe A Jihar Zamfara


‘Yan bindiga
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:00:15 0:00

Lokacin jana’izar wasu da ‘yan bindiga suka kashe.

Rahotanni daga jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya sun bayyana cewa an gudanar da jana'izar gomman mutanen da 'yan bindiga suka hallaka, bayan wani mummunan hari da suka kai a wasu kauyuka 4 a ranar Laraba.

Da maraicen ranar Laraba ne wasu shaidun gani da ido suka bayyanawa manema labarai cewa, sun kirga mutum 51 da aka kashe daga kauyuka 4 daga gundumar Magami ta karamar hukumar Dansadau a jihar Zamfara​.

Wannan mumunan lamarin dai ya afku ne kwana daya bayan da mutanen da suka rasa rayukansu suka yi yunkurin kai dauki ga mutanen garin 'Yar Doka, wadanda wasu bayanai ke cewa sun koma gida daga gudun hijira ne, kwatsam kuma ‘yan bindigan suka dirar musu da wannan kazamin hari.

Majiyoyi daga kauyukan da lamarin ya shafa sun ce ya zuwa daren jiya, mutane na cigaba da tserewa daga kauyukan yankin zuwa gudun hijira a Magami mai nisan kimanin kilomita 18.

Karin bayani akan: Bawar Daji, jihar Zamfara, 'Yan bindiga​, Nigeria, da Najeriya.

Shaidu sun bayyana cewa, mutanen da ‘yan bindigan suka kashe sun hada da akalla 20 daga kauyen Ruwan Dawa, sai wasu goma na Kangon Fari Mana, shida daga Madaba, wasu shida daga Arzikin, a yayin da kauyukan Mai Kogo da Mai Aya-aya da Mai Rairai, kowanne mutum biyu, sai Gidan Maza da Kunkelai mutum dai-daya kowannensu.

Wani shaida daga Kangon Fari Mana ya ce 'yan fashin sun shafe kimanin sa'o'i bakwai suna cin karen su ba babbaka tare da harbe-harben kan mai uwa da wabi.

Mutanen kauyen 'Yar Doka da suka nemi dauki daga makwabtansu, sun koma gida ne kwana daya kafin wannan kazamin harin, don ganin ko akwai halin noma gonakinsu kamar yadda bayanai suka bayyana.

A cewar mazaunan yankin 'yan bindigar sun dauki alkawarin cewa ba'za a yi noma ba a fadin gundumar Magami, kuma sun yi imanin cewa, wannan kuduri ne ya sanya su sake afka wa kauyen na 'Yar Doka.

Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle
Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle

Da safiyar nan ne za'a yi jana'izar mutanen kauyen Kangon Fari Mana su goma a garin Magami, inda mutanen kauyen suka bayyana cewa, ba za su iya yi wa 'yan uwan nasu sutura ba a can saboda fargabar maharan za su dawo a kowanne lokaci.

Baya ga mutanen da aka kashe, wani shaida ya ce an kai mutum 11 da aka jikkata a babban asibitin Magami inda suke ci gaba da samun kulawa daga ma’aikatan jinya.

Sun kara da cewa ba su da tabbaci ko an samu asarar jin rauni ko mutuwa a bangaren 'yan bindigar da suka addabi al’umman yanki "saboda yadda a yawancin lokuta su kan kwashi mutanensu ne su tafi da su."

Mazaunan 'Yar Doka dai sun koka da rashin samun dauki daga jami'an tsaro, lamarin da suka alakanta da yadda yankin nasu ke cikin lungu da kuma rashin isassun kayan aikin zamani na jami'an tsaro.

Sun ci gaba da cewa, jirgin yakin da suka hango daga bisani ma bai iya fatattakar maharan ba.

Idan za'a iya tunawa, a baya-bayan nan ne direbobin motoci da na baburan acaba a wasu garurruwan jihar Zamfara, musamman karamar hukumar Dan Sadau, suka gudanar da yajin aikin mako daya don bayyanawa gwamnati mawuyacin halin da suke ciki saboda karuwar tabarbarewa tsaro, bayan harbe wani direba tare da sace 'yan matan amaryar da ya dauko a yankin Mashayar Zaki.

ZAMFARA: Gangami akan neman kawo karshen kashe kashe
ZAMFARA: Gangami akan neman kawo karshen kashe kashe

Da muka tuntubi rundunar 'yan sandan jihar ta Zamfara,, cewa ta yi ta samu rahoton afkuwar harin, kuma rundunar ta tura karin jami'an tsaro a yankin.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG