Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Jana’izar Jarumi Sani Garba S.K A Kano 


Jana'izar Sani SK (Instagram/Aminu S Bono)

Sani Garba SK na daya daga cikin fitattun jarumai da suka yi zarra a fagen  fina-finan barkwanci da kuma fitowa a matsayin uba.

Rahotanni daga Kanon Najeriya na cewa an yi jana’izar jarumin Kannywood Sani Garba S.K wanda ya rasu a ranar Laraba bayan fama da rashin lafiya.

An gudanr ada jana’izar ne da misalin karfe tara na safe agogon Najeriya a unguwar Mandawari da ke jihar.

Marigayin ya kwashe wasu shekaru yana fama da rashin lafiya, lamarin da ya sa a aka dena ganinsa a fina-finai a ‘yan shekarun baya-bayan nan.

A watan Nuwamban da ya gabata, an yi ta yada jita-jitar cewa jarumin ya rasu, hakan ya sa ya fito kafafen sada zumunta ya musanta ikirarin.

In lokaci ya yi, ba sai an tsaya ana ta wani yamadidi ba, za a tafi, kuma kowa da ka gani zai dandana mutuwa. Muna fatan dai idan mun zo mutuwa Allah ya sa mu cika da imani.” Margayi Garb SK ya fada a watan Nuwamba a wani bidiyon da ya karade shafukan sada zumunta.

Sani Garba SK na daya daga cikin fitattun jarumai da suka yi zarra a fagen fina-finan barkwanci da kuma fitowa a matsayin uba.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG