Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Jana’izar Wasu Yara 8 Da Suka Mutu Sakamakon Zaftarewar Kasa A Kebbi


Zaftarewar kasa - Kebbi
Zaftarewar kasa - Kebbi

Yayin da jama'a ke ci gaba da alhinin ibtila'in da ya yi sanadin salwantar rayukan almajirai takwas a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya, gwamnatin jihar ta ce zata dauki matakin kare sake aukuwar hakan nan gaba.

Almajiran na makarantar Malam Dan Umma, sun hadu da ajalinsu ne a lokacin da kasa ta rufta a kansu a lokacin da suke ginar kasa a Dutsin Dukku, lamarin da masu kula da kare hakkokin yara suka ce bai dace a bari yara suna irin wannan aikin na karfi ba.

Dutsin Dukku da ke unguwar Badariya a cikin garin Birnin Kebbi a jihar Kebbi, ya kasance wurin da jama'a ke gino kasa domin amfani da ita.

Zaftarewar kasa - Kebbi
Zaftarewar kasa - Kebbi

Kwamishinan yada labarai na jihar Kebbi Yakubu Ahmad, yace wuri ne inda jama'a ke nema wa kansu sauki idan suna bukatar kasa domin yin ciko ko wani amfani na daban.

Samun kananan yara da hannu a harkar ginar kasa a wurin, abu ne da masu fafutukar kare hakkokin yara suka ce bai dace ba, domin ko bayan irin wannan ibtila'i da ya faru, yana da illoli ga rayukan yaran a cewar Rabi'u Bello Ghandi, na kungiyar' Save The Child Initiative.

Rundunar 'yan sandan Najeriya a ta bakin kakakinta a jihar Kebbi, Nafi'u Abubakar, tace tana gudanar da bincike akan faruwar wannan lamari.

Tuni dai aka yi jana'izar yaran su takwas, inda jama'ar gari ke cike da juyayi musamman ganin wannan shi ne karo na farko da aka samu haka.

Zaftarewar kasa - Kebbi
Zaftarewar kasa - Kebbi

Ita kuwa gwamnatin jihar tace ya zamo dole ta yi nazarin aukuwar lamarin kuma ta dauki matakin kare sake faruwar bala’in a nan gaba, kamar yadda kwamishinan yada labarai na jihar Yakubu Ahmad ya bayyana.

Yankewar kasa ko kuma mahakar ma'adinai ta binne mutanen da ke wurin, abu ne da ya sha faruwa a kasashen duniya kuma a lokuta da yawa ana samun salwantar rayuka.

Saurari rahoton Muhammad Nasir:

An Yi Jana’izar Wasu Yara 8 Da Suka Mutu Sakamakon Zaftarewar Kasa A Kebbi
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG