Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 9 Sun Mutu, 934 Sun Jikkata A Girgizar Kasa Mafi Karfi Cikin Shekaru 25 A Kasar Taiwan


Girgizar kasa mafi karfi cikin shekaru 25 ta afka kan kasar Taiwan, mutane 9 sun mutu, 934 suka jikkata, ana kuma ci gaba da neman mutane 50
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:34 0:00

Girgizar kasa mafi karfi cikin shekaru 25 ta afka kan kasar Taiwan, mutane 9 sun mutu, 900 suka jikkata, ana kuma ci gaba da neman mutane 50

Girgizar kasa mafi karfi a cikin shekaru 25 ta afku a yankin Taiwan a safiyar yau Laraba, inda ta kashe mutane tara, tare da sa wasu tserewa ta tsagar gine-gine da suka ruguje ta kuma dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa a daukacin tsibirin.

WASHINGTON, D. C. - Da farko dai an bayar da gargadin tsunami ce amma daga baya aka daga shi.

Girgizar kasar dai ta kasance ne a gabar tekun kauyen gundumar Hualien mai tsaunuka, inda girigizar kasar ta bar gine-gine a lankwashe a kusurwoyi maki 45, tare da murkushe benensu na kasa.

Girgizar kasa a Taiwan
Girgizar kasa a Taiwan

Sama da kilomita 150 kwatakwacin mil 93 a babban birnin kasar, Taipei, fale-falen buraka sun fado daga tsofaffin gine-gine, kuma makarantu sun kwashe dalibansu zuwa filayen wasanni, tare da basu kayan kariya. Wasu yara sun lulluɓe kansu da litattafan karatu don kiyaye abubuwa masu faɗowa yayin da girgizar ƙasar ke ci gaba.

Hotunan talabijin sun nuna makwabta da ma'aikatan ceto suna daga mazauna daga cikin buraguzo har da wani yaro ta tagogi zuwa kan titi, bayan da kofofin suka rufe a girgizar. Duk sun bayyana suna iya tafiya amma cikin kaduwa ba tare da munanan raunuka ba.

Taiwan
Taiwan

Mutane tara ne suka mutu a girgizar kasar da ta afku da misalin karfe 8 na safe, a cewar hukumar kashe gobara ta kasar Taiwan. Kamfanin dillancin labarai na United Daily News ya ba da rahoton cewa mahara uku sun mutu sakamakon zaftarewar duwatsu da aka yi a gandun dajin Taroko da ke Hualien, kuma wani direban motar dakon kaya ya mutu a Hualien din yayin da duwatsu suka afka wa motar.

Taiwan
Taiwan

Wasu karin mutane 934 ne kuma suka jikkata. A halin da ake ciki, hukumomi sun ce sun kasa gano mutane 50 a cikin kananan motocin bas a dajin kasar bayan girgizar kasar ta lalata hanyoyin sadarwar wayar. Wasu mutane shida kuma sun makale a wata ma'adanin kwal, inda ake ci gaba da aikin ceto.

Har ila yau girgizar kasar da kanan girgizar ta sun haddasa zabtarewar kasa guda 24 tare da lalata hanyoyi 35 da gadoji da kuma titunan karkashin kasa.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG