Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Jana'izar Mutanen Da Sojojin Kamaru Suka Kashe a Yankin Masu Amfani Da Inglishi


Sojojin Kamaru a garin da suka kai hari

Sojojin Kamaru sun afkawa wani otel a garin Pinyin dake yankin masu anfani da harshen Ingilishi inda suka kashe mutane 30 da suke zargin'yan tawaye ne ranar Alhamis da ta gabata

A kasar Kamaru, mutanen yankin dake magana da harshen Ingilishi, jiya Lahadi suka bizne ‘yan uwan su, su 30 da aka kashe a ranar alhamis din data gabata a garin Pinyin dake arewa maso yammacin kasar.

Sai dai kawo yanzu gwamnati bata fidda wata sanarwa game da wannan lamarin ba, amma mazauna garin sunce sojojin gwamnati ne suka afkawa wani hotel, suna cewa wai akwai wasu mutanen da yan aware ke garkuwa dasu a cikin hotel din.Mazauna garin suka ce sojojin sun harbe kusan duk wanda suka gani a hotel din a wannan lokacin.

Wakilin Muryar Amurka Moki Edwin Kindezeka ya aiko da rahoton yana cewa.

Daga cikin daruruwan mutanen da suke kukan mutuwar ‘yan uwansu har da wata baiwar ALLAH ‘yar shekaru 54 da haihuwa mai suna Angelica Maluh wadda ta gano gawar danta dan shekaru 24 cikin wadanda aka kashen.

Tace bata san wane irin kaddara ne ya fada musu ba haka da ake kashe diyan su kamar kuda, tace ta bar kome a hannun Allah wanda shi kadai ne zaiyi muna sakayya tare hakunta wadanda suka aikata wannan danyen aikin.

Tace amma ita tasan dan ta bai aikata laifin da yakai na a kashe shi yana dan matashin sa ba.

Rikici dai ya barke ne a Kamaru yankin da ake Magana da harshen turanci dake arewa maso yammaci da kuma kudu maso yammaci a cikin shekarar 2016 lokacin da malamai da lauyoyi a yankin suka gudanar da zanga-zangar abinda suka kira wariya da danniyar da suka ce yankin masu Magana da faransanci suke musu, wannan ne fa ya haifar da kiraye-kirayen ballewa daga kasar.

Wannan yunkurin nasu yasa a cikn watan nuwambar shekarar 2017 shugaba Paul Biya ya kaddamar da yaki akan wadannan mutanen masu neman ballewa inda ya kira su ‘yan taadda.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG