Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Kira Ga MDD Ta Dauki Mataki Kan Karuwar Kyamar Musulunci


Imran Khan

Fara ministan Pakistan Imran Khan ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya MDD, da ta haramta abin da ya kira kyamar musulunci a kasashe masu yawa, ciki har da kasar India.

A jawabin da ya gudanar ta hoton bidiyo a babban zauren MDD ranar Juma’a, shugaban na Pakistan ya yi Allah wadai da da wani zanen batanci ga Annabi Muhammadu (SAW) da gidan jaridar Charlie Hebdo na kasar Faransa ke fitarwa duk mako.

“Ana ci gaba da kaiwa musulmi hari ba tare da daukar hukuncin ba a kasashe masu yawa,” Khan ya fadi. ya kuma kara da cewa karuwar nuna tsana ga addinai da tashin hankali ta hanyar amfani da cewa ‘yancin magana ne ya kara haddasa kyamar Islama.

Khan ya sake zargin gwamnatin Fara Ministan India Narendra Modi da mayar da kasarsa kasar dake goyon bayan tsanar addini da tashin hankali ga kusan tsirarun musulmai miliyan 200 dake zaune a India.

Wakilin India a Majalisar Dinkin Duniya, T.S. Tirumurti, ya shiga shafin Twitter ya yi Allah wadai da jawabin Khan, ya kiran jawabin da wani sabon salon kankanci na diplomasiyya wanda ke ciki da karya.

Facebook Forum

An Ga Watan Azumi A Najeriya - Sultan

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammada Sa'ad Abubakar Ya Ba Da Sanrwar Ganin Watan Ramadan
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

An Kai Wa Ofisoshin Kungiyar Ba Da Agaji Hari A Arewa Maso Gabashin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:02 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG