Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Kabilanci Na Ruruwa a Iraqi


Gwamnatin Kurdawa ta Iraqi na gargadin hauhawar rikice-rikicen kabilanci a kasar da ake takaddama kan wasu yankuna, ta na cewa Larabawa na tilastawa iyalan Kurdawa suna barin gidajensu ta hanyar da ke barazana ga zaman lafiya.

Masana harkokin tsaro na cewa dawo da rikicin kabilanci kan takaddamar mallamar gidaje a Kirkuk, zai iya share fage ga kungiyar IS ta kai hare-hare ganin cewa har yanzu akwai burbudin ‘yan kungiyar a lardin dake da mabanbantan kalibu da arzikin Man fetur.

A wata sanarwa da ya fitar, Fara ministna yankin Kurdawa Masrour Barzani ya kwatanta yinkurin korar Kurdawa da yake faruwa da kudurin tsoron shugaban kasar Iraqi Sadddam Hussain, wanda ya yi kokarin kawar da kabilar Kurdawa.

“Muna kallon abin da ke faruwa cikin matukar damuwa a yankunan da ake takaddama akai musamman ma Lardin Kirkuk, inda aka yi yunkurin sauya mazauna yankin, tsarin da har yanzu yake aiki,” a cewar Barzani.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG