‘Yar majalisar wakilan Amurka, Ilhan Omar ta kafe wani sako a shafinta na Twitter a daren jiya Laraba, inda ta nuna wani hotonta a dakin majalisar wakilan kasar, ta kuma rubuta sako zuwa ga shugaba Trump da magoya bayansa, wadanda cikin ‘yan kwanakin nan suka sha nuna cewa matar, wadda ba ba-Amurkiya bace, ta koma Somalia kasarta ta asali.
Omar ta rubuta, “Ina inda ya kamata in kasance, wurin da nake wakiltar jama’a, sai kusan yadda zaku yi."
Wannan sakon na zuwa ne bayan da Trump, ya caccaki Omar da wasu mata 3 da ba turawa ba, dake majalisar tarayyar kasar kwanaki hudu a jere, yana ci gaba da jefa alamar tambaya akan ko suna kishin Amurka yana kuma nuna cewa su bar kasar.
“Ina gani kamar ba sa son Amurka,” abinda Trump ya ce kenan akan ‘yan majalisar Ilhan Omar, Alexandria Ocasio-Cortez, Ayana Pressley da kuma Rashida Tlaib.
Za ku iya son wannan ma
-
Janairu 25, 2023
Mawakiya Yar Najeriya Ta Yi Tarihi A Bikin Bada Lambar Yabo Na Oscar
-
Janairu 13, 2023
Lisa Marie Presley, Diyar Mawaki Elvis Ta Rasu
-
Janairu 11, 2023
Ana Tsaftace Yankunan Da Mahaukaciyar Guguwa Ta Ratsa A California
Facebook Forum