Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Zanga-zanga Kan Fim Din 'Lady Of Heaven' A Birtaniya Saboda Zargin Batanci Ga Islama


Wasu masu zanga zanga

Fim din Lady Of Heaven, wanda wani malamin Shi'a Sheikh Yasser al-Habib ya rubuta kuma Eli King ya ba da umarni, ya kwatanta labarin Nana Fatima ne, 'yar Annabi Muhammad SAW.

Wasu da dama dai sun ce fim din na cike da sabo kuma sun ce yana yada labaran karya kan addinin Musulunci.

Burtaniya na ta ganin tashin hankali game da wani fim din - The Lady of Heaven wanda masu sukar suka kira "mai cike da sabo" da "wariyar launin fata".

Jaridar Firstpost ta ruwaito cewa Fim din, wanda aka sake shi a ranar 3 ga watan Yuni, ya nuna labarin Nana Fatima, 'yar Annabi Muhammad (SAW,) kuma an sanya shi a matsayin fim na farko da ya fara yin haka.

Wannan labarin yana da alaƙa da tatsuniyar wani ƙaramin yaro dan Iraqi a zamanin yau bayan shekaru 1,400 da suka wuce.

Sai dai, sanannen silima a Burtaniya ya takaita duk wani nunin fim din saboda damuwa ga ma'aikatansa da amincin abokan cinikayyars. Haka kuma, Maroko ta haramta fim din, yayin da Masar, Pakistan, Iran da Iraki duk suka yi tir da shi.

Fim din ya kai ga cire wani limami wanda ke matsayin mai ba gwamnati Burtaniya shawara.

Fim din dai ya sha kakkausar suka daga al'ummar Musulmi, inda da dama suka ce fim din na cin mutunci ne da kuma nuna wariyar launin fata.

Daya daga cikin dimbin matsalolin da fim din ke da shi shi ne yadda ake nuna annabawan Musulunci.

Haka kuma an an yi suka sosai kan fim din saboda yadda yake nuna wasu jarumai da dama a matsayin Sahabban Annabi Muhammad SAW, wadanda suka hada da Abubakar, Umar ibn al-Khattab, Kalifofin Musulunci na farko.

~Firstpost

Dubi ra’ayoyi

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG