Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yiwa Manyan Sojojin Najeriya Ritaya


Wasu sojojin Najeriya

Rahotanni daga Najeriya na cewa rundunar tsaron kasar, ta yiwa wasu manyan sojojin kasar ritaya.

An musu ritayar ne bayan da aka samu hannun wasu a zaben shekarar 2015 da ya gabata yayin da wasunsu kuma aka same su da laifi a badakalar sayen makamai.

Majalisar rundunar sojin kasar ce ta ba da umurnin yin hakan bayan da aka gudanar da bincike.

A hirarsu da Muryar Amurka, Kakakin rundunar sojin kasar, Kanal Sani Usman Kuka Sheka, ya ce wasu daga cikinsu sun gurfana a gaban hukumar EFCC da ke yaki da masu yiwa arzikin kasa zagon kasa.

Ya kuma kara da cewa wannan mataki da aka dauka, yanayin aikin sojin ne ya ba da damar yin hakan.

Domin jin cikakken rahoton da kuma irin mukaman sojojin da aka yiwa ritaya, saurari rahoton Hassan Maina Kaina daga Abuja:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:18 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG