Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram Ta Halaka Sojojin Nijar Da Najeriya a Diffa


Sojojin Najeriya bayan da suka fatattaki 'yan Boko Haram daga wani sansaninsu dake dajin Sambisa a Jihar Borno

Wani hari da aka kai barikin soji da ke Boso a yankin Diffa na Jamhuriyar Nijar, ya yi sanadin mutuwar sojoji 34, bayan da wasu mahara da ake tunanin ‘yan Boko Haram ne suka kai hari a sansanin soji.

Hukumomin Nijar sun ce daga cikin wadanda suka mutu har da sojojin Najeriya biyu.

Wadanda suka shaida lamarin sun gayawa Muryar Amurka cewa baya ga harin da suka kai a sansanin sojin 'yan kungiyar ta Boko Haram sun kuma kona barikin baki daya.

"Muna shiga sai muka ga mutanen da aka karkashe kawai ba mu tsaya ba sai muka fita." Inji wani mazaunin yankin garin na Boso da ya nemi kada a ambaci sunansa.

Jamhuriyar Nijar da ke makwabtaka da Najeriya ita ma ta shiga fama da matsalar tsaro tun bayan da 'yan kungiyar ta Boko Haram suka fara kai hare-hare a yankin tafkin Chadi.

Domin jin cikakken bayani kan wannan hari saurari hirar da wakiliyar Muryar Amurka Tamar Abari ta yi da wani mazaunin yankin da kuma rahoton da Sule Mumuni Barma ya aiko mana:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:49 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG