Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An zargi shugaba Jonathan da kin bin shawara game da batun ahuwa


Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

An zargi Shugaba Jonathan da kin bin shawarar da Shugabannin Arewa suka bashi dangane da batun ahuwa

Daya daga cikin shugabannin Dattawan Arewa (Arewa Consultative Forum) Lauya Dalong ya ce Shugaba Jonathan bai bi shawarwarin da suka bashi ba.

Ya ce sun fada masa cewa mambobin kwamitin neman sulhun kada su wuce nutane 16 wadanda zasu hada da Kiristoci daga kudancin Najeriya. Kana daga Arewa Kristoci da Musulmai su samu mambobi dai-dai. Amma kuma duk mutanen da za'a zaba su kasance ba wadanda suka yi fice ba ne a kasar ko ta wane fani. Sai dai su zama masu gaskiya da adalci kuma basu da son kai. Ya kara da cewa duk mambobin kwamitin, musamman shugabanta ya kasance wanda 'yan Najeriya suka yadda da shi, 'yan kungiyar Boko Haram sun yadda da shi kuma sun tabbatar zai iya biya masu bukata.

Sai dai a wani hannun kuma Sule Baban Nana wani tsohon sakatare a jihar Gombe ya ce bai ji dadin guje ma kwamitin da Dr Datti da Malam Shehu Sani suka yi ba. Yace ko menene dalilinsu tun da abun ya shafi zaman lafiyar Arewa to kamata ya yi su amshi nadin da aka yi masu, su taimaka a kawo karshen tashin tashinar da suka addabi nahiyar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:41 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG