Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Binciken Kisan Da Aka Yiwa Wata Mata


wasu 'yan sandan majlisar dokokin Amurka na kallon motar matar da aka kashe ranar 3 ga watan oktoba

Sunan wadda aka kashe Miriam Carey kuma shekarun ta 34

Hukumomin kasar Amurka na ci gaba da kokarin gano dalilin da ya sa wata mata dauke da 'yar ta a cikin mota ta yi yunkurin kara motar ta, ta, da wani shingen tsaro a fadar shugaban kasa ta White House, wanda hakan ya sa 'yan sanda suka bi ta a guje da motocin su karshen ta suka harbe ta har lahira a kusa da majalisar dokokin Amurka.

Mahaifiyar ta mai suna Idella Carey ta ce sunan matar Miriam Carey kuma shekarun ta 34. Mahaifiyar ta shaidawa gidan talbijin din ABC cewa 'yar ta, ta yi fama da matsalar rashin lafiya mai nasaba da kunci da damuwa bayan haihuwar 'yar ta a cikin watan agustan da ya gabata, wadda da turanci a ke kira Postpartum Depression.

Majiyoyin 'yan sanda sunce matar ta na da tarihin tabun hankali kuma a cikin kan ta, ta na jin kamar shugaba Barack Obama ya na yi ma ta magana.

'Yan majalisar dokoki da ma'aikatan majalisar sun yi awa daya a killace a wani daki a lokacin da abun ke faruwa a ranar alhamis, amma 'yan sanda sun ce babu wata barazanar da aka yiwa 'yan majalisar dokokin daga cikin ginin majalisar.

Hukumomi sun ce jami'an 'yan sanda biyu sun ji ciwo kuma ana kyautata cewa za su samu sauki. Kuma ba sa jin cewa al'amarin ya na da nasaba da matsalar rufe wasu ma'aikatun gwamnatin da ake fama da ita yanzu haka a kasar Amurka.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG