Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kalubalen Daliban Najeriya Da Suka Karanci Aikin Likita A Ketare


Likitoci da maikatan asibiti suna duban mai ciwo
Likitoci da maikatan asibiti suna duban mai ciwo

Masu ruwa da tsaki a fannin Lafiya na Najeriya sun nanata muhimmancin kafa cibiyoyin ba da horo na musamman ga daliban da suka kammala karatun aikin likita a jami’o’in kasashen waje.

Bayanai sun nuna cewa daliban Najeriya da dama da suka karanto aikin likita a jami'o'in kasashen waje na fuskantar kalubale a yayin rubuta jarabawar neman lasisin aikin likita da hukumar kula da ayyukan likitoci ta Najeriya take shiryawa.

Bayan kammala karatun su a jami’o’in kasashe daban-daban na duniya, dalibai 836 ne suka rubuta jarabawar neman lasisin aikin likita a makon da ya wuce, wadda hukumar MDCN mai kula da ayyukan likitoci a Najeriya ta shirya a Asibitin koyarwa na Aminu Kano.

Sakamakon jarabawar ya nuna kashi 40 da doriya na adadin daliban ne suka yi nasara a jarabawar, yayin da sauran kashi 60 cikin 100 kuma suka fadi.

Dr Abdullahi Kabir Sulaiman shine shugaban kungiyar likitocin Najeriya reshen jihar Kano, ya kuma bayyana wasu daga cikin dalilan daukar tsaurara matakai wajen shirya jarabawar,

Ya ce "shi aikin likita yana da muhimmanci sosai saboda rai guda daya ne, idan mutum ya rasa shi shike nan, idan wani bangare na mutum ya baci ko ya nakasa ba dole ba ne a iya gyara shi ya koma kamar yadda yake a baya, shine ya sanya aikin likita ba’a wasa dashi”

A wani mataki na tabbatar da sahihanci ko ingancin likitocin jami’o’in da ‘yan Najeriya ke halarta a ketare, hukumar MDCN ta so ta kirkiro wani tsarin ba da horo na musamman ga daliban da suka kammala karatun aikin likita a kasashen waje gabanin a basu damar rubuta jarabawar samun lasisi, amma yunkurin ya ci tura, a cewar Farfesa Auwalu Umar Gajida, mataimakin shugaban Asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano.

“Shekaru biyu da suka wuce hukumar ta bullo da tsari inda za’a rika basu wannan horon, amma da iyayen yara da su daliban suka ga kamar ko ba’a kyauta musu ba ne har maganar ta kai majalisar dokoki ta kasa, aka kirawo shugabannin wannan hukuma suka je majalisa suka yi bayani, kuma daga baya majalisar ta ce su dakatar da wannan tsari na ba da horo na bai daya.”

Dr Abdullahi Kabir ya yi karin haske akan yadda aka tsara ba da horo na musamman din ga daliban da su suka kammala karatu a ketare.

Ya ce "za’a koya musu cutukan da suka fi yawa a nan, kamar ciwon hawan jini, zazzabin Malariya da kyanda. za’a koya musu yadda za su yi, don haka idan aka zo rubuta jarabawar dalibi ya san abin komai zai zo da sauki”.

Wasu daga cikin kasashen da ‘yan Najeriya ke tura ‘yayansu domin karatun aikin likita sun hada da Ukraine da Sudan da Cyprus, India, Masar, Rasha, Hungary, Belarus da kuma Guyana.

Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG