Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ce-ce-ku-ce Kan Binciken Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Kano


KANO: Dr. Abdullahi Umar Ganduje gwamnan Kano

Zargin cewa hamshakin mai kudin nan da ya fi kowa arziki a nahiyar Afrika wato Aliko Dangote, ya ba da wasu miliyoyin kudade domin a yi watsi da binciken da majalisar ta sa a gaba kan masarautar Kano ya bar baya da kura.

Jama’a a Kano na ci gaba da bayyana ra’ayi dangane da matakin majalisar dokokin jihar na kafa kwamitin bincike akan tsohon shugaban majalisar Kabiru Alhassan Rurum game da zargin sa da karbar naira miliyan 100 a matsayin toshiyar baki daga hannun Alhaji Aliko Dangote.

Rahotannin sun yi zargin cewa Dangote ya ba da toshiyar bakin ne domin majalisar jihar ta jingine bincike akan Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu kan yadda ake tafiyar da kudaden masarautar.

Ko da yake mukarraban Dangoten sun musanta hanunsa a wannan lamari.

Masu lura da al'amura sun ce kakakin majalisar ya sauka daga mukaminsa ne domin ya kaucewa shirin tsige shi da aka yi bayan da ya dawo daga umra.

Tuni dai aka nada shugaban masu rinjaye Yusuf Ata dake wakiltar mazabar Fagge a matsayin sabon kakakin majalisar.

Yayin hada wannan rahoto, al'umar jihar Kano na ci gaba da bayyana ra'ayinsu dangen da wannan takaddama musamman ma kan abinda ya shafi kwamitin binciken da aka kafa, kamar yadda za ku ji rahoton da wakilinmy Mahmud Ibrahim Kwari ya aiko mana daga Kano:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00

Facebook Forum

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG