Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihar Jigawa Ta Gudanar Da Zabe Duk Da Kotu Ta Hana


Ma'aikatan zabe

Hukumar zaben jihar Jigawa ta gudanar da zabe a jihar Jigawa bayan kotu ta bada umarnin a dakatar da zaben.

Yau hukumar zaben Jigawa ke gudanar da zaben shugabannin kanananan hukumomin jihar 27 da kuma kansiloli 284 a fadin jihar.

Hukumar tace Jam’iyyu 10 ne ke fafatawa a zaben, amma Jam’iyyar PDP dake zaman babbar Jam’iyyar hamayya tace ba zata shiga zaben ba saboda girmama umarnin alkalin babbar kotun tarayya dake Dutse wanda ya bada odar dakatar da zaben har sai bayan ya saurari korafin da ‘yan takarar jam’iyyar suka shigar gaban kotun.

Barrister Yakubu Abdullahi Ruba, jagoran Lauyoyin da suka shigar da kara na kalubalantar matakin hukumar zabe ta Jigawa kan cire sunayen mutanen da jam’iyyar PDP, ta fitar daga jerin ‘yan takaran shugabanin kananan hukumomi da Kansiloli ya ce domin girmama wancan umarni ne jam’iyyar ta PDP ta yanke hukuncin kauracewa zaben.

Shugaban hukumar zaben na jihar Jigawa Alhaji Sani Muhammad, yace hukumar ta dogara da sahihan hujjoji da kuma shawarwarin da ta samu ne daga Lauyoyinta gabanin ci gaba da gudanar da zaben.

Tun da safiyar asabar din nan ne dai jami’an hukumar zaben suka bayana a tashoshi da runfunar zabe dake sassan jihar Jigawa sai dai an fuskanci karancin masu fita jefa kuri’a.

Wani Lauyaya mai zaman kansa Barrister Abdullahi Bulama, yace ta fuskar shara’a in dai har umarnin kotu ya tabbata cewa kotu ta sa a dakatar ko kuma a bi wasu ka’idoji kafin ayi amma ba a yiba wannan zabe haramtatcen zabe ne.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG