Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Hannu A Rikicin Tsaunin Mambila Zasu Fuskanci Fushin Gwamnati


Abdulrahman Dambazau

Gwamnatin Najeriya ta sha alwashin bi wa jama’a da suka yi hasarar ‘yan uwa da dukiyoyi sakamakon tashe-tashen hankalin da ya barke a tsaunin Mambila hakkin su.

Ministan ma’aikatar cikin gida na Najeriya Alh. Abdulrahaman Dambazau ya bayana cewa gwamnati za ta bi wa jama’ar da suka yi hasarar sakamakon tashe-tashen hankula da ya barke tsakanin mazauna yankin tsaunin Mambila na karamar hukumar Sardauna dake jihar Taraba, hakkin su.

Ministan wanda ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya da ta kai ziyarar gani da idon irin barna da tashin hankalin ya haddasa da kuma halin rayuwa da mutanen da rikicin ya tilastawa barin gidajensu ke ciki ya bayyana duk wanda bincike ya samu da hanu zai fuskanci fushin hukuma.

A ganawar minista Abdulrahaman Dambazau da shugabannin bangarorin da ke fada da juna, na addini da masu ruwa da tsaki na yanki, ya ce sun fahinci rikicin ya samo asali daga takaddama kan rabon gonaki da filayen kiwo wanda ya ce na bukatar zama kan teburin tattaunawa don warware matsalar da wanzar da dawamammiyar zaman lafiya.

Tashe-tashen hankulan da yankin tsaunin Mambila ya fada a ciki baya-bayan nan ba zai rasa nasaba da rashin raba dai dai na albarkatun kasa sakanin al’umomi mazauna yankin da kuma rashin daidaito na wakilci ga kowane bangare a harkokin gudanarwa na yankin inji shugaban kwamitin amintattu na kungiyar rayawa ta Hausa-Fulani Alh. Bakari Mohammed Tamya.

Tashin hankali na bayan nan kuma mafi muni shine na huda cikin shekaru arba’in da bakwai idan aka kwatanta adadin mutane da suka rasa ransu, gidaje da aka lalata, hasarar dukiyoyi da kuma mutane sama da dubu hudu da suka yi hijira dake fama da matsalar karancin abinci da wuraren kwana musamma a lokaci da damina ta kama.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG