Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnoni A Najeriya Na Kara Juya Akalar Siyasar 2023


Buhari da Sanata Abdullahi Adamu da Mai Mala Buni
Buhari da Sanata Abdullahi Adamu da Mai Mala Buni

Gwamnoni na ci gaba da daukar matakai don xjuya akalar babban zaben Najeriya a shekarar 2023.

Tuni har wasu daga gwamnonin musamman a APC su ka zabi daya daga manyan masu neman tikitin jam’iyyar.

Dama ko da kada kuri'a za a yi a zaben fidda gwani, gwamnoni na da tasiri kan wakilan da a kan tara don zaben.

Wannan ya sa manyan 'yan takarar ke zama da gwamnonin don neman goyon bayan su da hakan ke nuna samun goyon bayan gwamna tamkar samun jihar ce gaba daya.

Masanin harkokin siyasa Dr.Abubakar Kari ya ce ba lalle ne iyayen siyasa su hana mabiyan su fitowa takara ba don salon zaben 2023 na daban ne.

Kari na magana ne kan fitowar Osinbajo alhali ga maigidan sa Tinubu a takarar.

Fadar gwamnatin ta bakin Garba Shehu ta ce sam ba a samu baraka a taron APC ba inda sauran 'yan takarar fadar ba su samu nasara ba sai 'yan takarar gwamnoni.

Ba alamun za a yi zaben APC na fidda gwani da kada kuri’a in an duba yanda jam’iyyar ta karkata ga daidaitawa amma PDP ka iya zuwa ga kada kuri'a don barin kofar takara bude.

Ga dai rahoton Nasiru Adamu El Hikaya daga Abuja:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

XS
SM
MD
LG