Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Tsaro Sun Ceto Wasu Matukan Jirgin Ruwa Daga Hannun 'Yan Fashi A Somaliya


Jami’an kasar Somaliyya sun ce mayakansu sun ceto matukan jirgin ruwa guda takwas na kasar India da wasu ‘yan fashin teku suka kwacewa jirginsu, suka kai su bakin gabar teku a shekaranjiya Litinin.

Magajin garin Hobyo, Abdullahi Ahmed Ali, ya fadawa sashen harshen Somaliyya na Muryar Amurka yau Laraba cewa matukan jirgin ruwan mai lamba MSV AL Kauser na nan lami lafiya a hannun jami’an tsaro.

Magajin garin ya kuma ce jami’an tsaro na tsare da ‘yan fashin tekun da suka yi garkuwa da matukan jirgin bayan da suka fidda su daga cikin jirginsu a wajen gabar tekun Hobyo.

An kuma gano wasu matukan jirgin su biyu a jirgin da aka sace bayan da jami’an tsaron suka gano shi a safiyar litinin, jimlar matukan jirgin ya kama goma kenan.

Ranar daya ga watan nan na Afrilu ne ‘yan fashin suka cafke jirgin a gabar tekun Somaliyya a lokacin da jirgin ke jigilar kayayyaki zuwa garin Kismayo.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG