Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Cigaba da Kone-Kone da Kisan Sari ka Noke a Jihar Benue


Kone-kone a jihar Benue.
Kone-kone a jihar Benue.

Rikicin jihar Benue yayi sanadiyar rasa rayuka da dukiyoyi na miliyoyin Nairori,tsakani Fulani da Tiv.

Ana samu cigaba da kone-kone da kisan sari ka noke a wasu sassa na jihar Benue batan wani rikici daya afku a wurare da dama a jihar.

Rikicin yayi sanadiyar rasa rayuka da dama da kuma dukiyoyi na miliyoyin Nairori a jihar inda rikicin ya rutsa da wadanda basu ci ba basu sha ba.

A wani hira da wakiliyar mu tayi da wata yar kabilar Tiv Naomi Iken tace duk da samu saukin tashin hankali a wasu wurare, har yanzu ana kone-kone a wasu wurare.

Ta kuma bada shawara cewa yakamata gwamnati kara kokari domin gani cewa ta shawo kan rikice-rikicen.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:28 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG