Accessibility links

A'ummomin Berom da Filani a Jihar Filato Sun Shirya Su Kawo Daidaituwa Tsakaninsu


Gwamnan jihar Filato

Filani da Berom sun dade suna kai ma juna hari a jihar Filato kuma sun sha yin alkawarin kawar da sabanin dake tsakaninsu. Watakila lokaci yayi yanzu da zasu kaiga daidaituwa.

Berom da Filani a jihar Filato sun bayyana cewa kofofinsu a bude suke domin sasanta sabanin dake tsakaninsu.

Wannan sabon yunkurin ya biyo bayan wasu hare-hare da aka kai a kananan hukumomin Barkinladi da Riyom kwanan nan lamarin da ya yi sanadiyar rasa rayuka da dama da kuma salwantar dimbin dukiya.

Shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen jihar Filato Useni Boro yace duk da sun yi asarar dukiyoyi da yawa a shirye suke su tattauna domin su samu fahimtar juna a tsakanin kabilun biyu. Yace an kashe masu yara biyu an kuma sace shanu 530. Yace kashe-kashe da sace sace za'a iya kawar da su idan an samu daidaituwa. Yace a wurinsu sasantawa ba abu mai wuya ba ne idan aka daina sace masu dabbobi. Da zarar an daina sace masu dabbobi da daina kashe masu yara zasu sasanta. Amma ya dorawa hukuma laifi domin duk wadanda aka kama a bangarorin biyu ana sakesu mai makon a hukuntasu.

Shugaban matasan Berom na kasa Rwang Dangtong yace a shirye suke su daidaita da Filani. Yace Filani da sojoji sun shiga kauyen Torok sun kone gidaje fiye da dari. Wasu ma da suke cikin dakunansu da wuta ta tashi sojoji sun tilasta masu su koma cikin dakunansu inda suka kone mururus. A wanan harin akalla mutane goma suka rasa rayukansu. Yace hare-haren sai yaduwa su keyi. Ban da haka suna samun wasiku ana ambata wuraren da za'a kai hari. Yace su dai suna hannun Allah. Yace sojoji suna taimakawa Filani su kashesu. Yakamata gwamnati ta yi wani abu a kai. Yace su basu ki sulhu ba. Kofarsu na bude. Su zo su tattauna. Yace su fada masu damuwarsu da tabbacin cewa zasu iya magance matsalar.

XS
SM
MD
LG