Accessibility links

Gwamnatin Jihar Benue ta Musanta Zargin Cewa ta Kori Filani daga Jihar


Gwamnan jihar Benue Gabriel Suswan

Bayan fadan da ya sake aukuwa tsakanin Tiv da Filani a jihar Benue an zargi gwamnatin jihar da korar duk ilahirin Filani dake cikin jihar zargin da yanzu gwamnatin ta musanta

Gwamnatin Jihar Benue ta musanta cewa tana kokarin korar al'ummar Filani daga jihar.

Kungiyar Filani wato Miyetti Allah ta yi zargin cewa gwamnatin jihar Benue tana kokarin ganin bayan al'ummar Filani dake zaune a jihar.

Mai ba gwamnan jihar shawara a kan labarai Dr. Cletus Akwaya ya musanta zargin wanda yace bashi da tushe balantana makama. Yace a yanzu akwai Filani da yawa zaune a jihar illa iyaka akwai rikici tsakanin Filani da manaoman jihar. Amma babu wani shiri na korar Filani daga jihar. Yace lamari ne a tsakanin bangarorin biyu, wato Filani da manoma kuma abun ya dauki tsawon lokaci.

Dangane da abun da gwamnatin jihar ke yi domin shawo kan rikicin da ya lakume rayuka da dama da dimbin dukiyoyi, Dr Akwaya yace gwamnatin jihar ta gana da shugaban kasar Najeriya inda ta roki a turo jami'an tsaro domin shawo kan lamarin da kuma tabbatar da tsaron lafiyar jama'a da dukiyoyinsu.

Dama can an kafa wani kwamitin sulhu na gwamnati da Sarkin Musulmi amma ba'a san irin tasirin da kwamitin din ya yi ba. Dr Akwaya yace gwamnatin Benue da fadar Sarkin Musulmi suka kafa shi kuma sarkin Gombe ne ke shugabantar kwamitin. Amma yace kwamitin bai samu damar mika rahotonsa ba.

Kan rasa rayukar da aka yi Dr Cletus Akwaya yace basu da adadin wadanda suka mutu saboda lamarin ya dade ana yi. Yace da Filanin da manoman duk sun tafka asara ta rayuka da dukiyoyi a rikicin.

XS
SM
MD
LG