Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Dakon Sakamakon Zaben Shugaban Kasar Mali


Shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita

An fara kidayan kuri'u a zaben shugaban kasa da aka yi jiya Lahadi a Mali, inda rahotanni ke cewa an samu tarzoma da hare-hare da aka kai da rokoki da barazana, da kuma kafa rumfunan zabe na bogi.

Al'umar kasar Mali na dakon sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar Lahadi.

Shugaba Ibrahim Boubacar Keita, yana neman wa'adi na biyu inda ya ke karawa da wasu 'yan takara 24 da suke kalubalantar shi.

Rahotanni sun ce masu jefa kuri'a ba su fito ba sosai a duk fadin kasar, ciki har da Bamako babban birnin kasar.

Rabin masu zabe a yankunan kasar biyu ne suka sami katunan zabe, ma'ana fiye da mutane 800,000 ba su sami damar kada kuri'a ba.

An dakatar da zabe a wani kauye da ke arewacin kasar, bayan da mayakan sa-kai suka harba rokoki kusa da wani ofishin Majalisar Dinkin Duniya.

Sai dai rahotanni suka ce babu wanda ya jikkata.

Rahotanni sun ce a wasu kauyuka da dama an doki malaman zabe, aka kona akwatunan zabe, wasu gungun mutane dauke da makamai sun hana turawan zabe shiga rumfunan zabe.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG