Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Gina Masallacin Da Yafi Kowanne Girma A Duniya


Masu Gina Masallaci

Rahotanni daga kasar Algeria na cewa kasar zata gina katafaren masallacin da ba irin sa a duniya a wajen girma, domin ya zame wa kungiyoyin Musulmi masu matsanci ra’ayi wani babban kalubale.

Kanfanin dillacin labarai na kasar Faransa AFP ta ruwaito cewa masallacin na Djamaa El Djazir za a gina shi ne a tsakanin wani yanki dake tasowa a fannin yawon bude ido da wata tsohuwa gunduma da a can da take zaman matattaran kungiyoyin ‘yan tsageran addini.

Ahmed Madani mai baiwa ministan harkokin gida shawara, wanda shine keda alhakin gina masallacin, ya shaidawa APF cewa da farko wasu sun soki lamirin su cewa gwamnati na gina wa wasu masu raayin rikau wurin ibada ne, amma akashin gaskiya Hukuma na gina wannan masasllacin ne don ya zama babban kalubale ga irin wadanan kungiyoyin.

An dai kiyasta cewa masallacin zai lakume kudi har dalar Amurka milyan dubu da milyan 400, kuma abubuwan da za a samar cikin sa zasu hada da dakin karatu da zai iya daukar littafai har miliyan guda, da makarantar al’kurani,da dakin adana kayan tarihi, da kuma Hasumiya mafi tsawo a duniya mai tsawon mita 265, da kuma farfajiyar masallacin da zata iya kwashe mutane dubu 120 a lokaci guda.

Madani yace anasa ran a kammala ginin wannan masallacin cikin shekara mai zuwa.

Shugaba Joe Biden ya zama Shugaban Amurka na 46

Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris

BIDIYO: Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:51 0:00

An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris

BIDIYO: An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46
please wait

No media source currently available

0:00 1:45:22 0:00
XS
SM
MD
LG