Accessibility links

Mace 'Yar Afirka Ta Farkon Da Ta Taba Samun Kyautar Nobel Ta Mutu

  • Halima Djimrao-Kane

Wangari Maathai ta kasar Kenya wadda ita ce mace ta farkon da ta taba samun kyautar yabon Nobel a fannin zaman lafiya, a nan a jami'ar Nairobi ne ranar 8 ga watan Maris shekarar 2010 lokacin da ta halarci wani taron tattaunawa

Wangari Maathai ta kasar Kenya da ta taba samun Kyautar Nobel Ta Mutu a birnin Nairobi ta na da shekaru 71

Wangari Maathai ‘yar kasar Kenya wadda ita ce mace ta farko a Afirka da ta taba samun kyautar yabon Nobel a fannin zaman lafiya, ta mutu ta na da shekaru 71.

Kungiyar da ta kafa mai suna “The Green Belt Movement”, ita ce ta bada labarin cewa Maathai ta mutu jiya lahadi a wani babban asibitin Nairobi bayan ta dade ta na jiyyar cutar sankara.

A shekarar 2004 kwamitin bayar da kyaututtukan Nobel ya karrama ta saboda tsayin dakar da ta yi ta fafata da tsohuwar gwamnatin kasar Kenya mai danniya da kama karya sannan kuma ta karfafawa mata guiwar kyautatawa kan su rayuwa.

A shekarar 1977 Maathai ta kafa kungiyar “The Green Belt Movement” domin ta taimakawa matan yankunan karkara su biyawa kan su bukatun su wajen samarwa kan su itacen dahuwa da abinci da tsaftataccen ruwan matsarufi ta hanyar yin amfani da wani shirin shuka itatuwa. Daga bisani shirin ya bunkasa ya hada har da maida hankali kan batutuwan demokradiya da kare hakkokin bil Adama da hakkokin mata da kuma zaman lafiya.

Kungiyar ta ce, ta tattara dubban daruruwan maza da matan da su ka shuka itatuwa fiye da miliyan 47.Haka kuma Wangari Maathai ta yi zama ‘yar majalisar dokokin kasar Kenya, sannan kuma ta rike mukamin mataimakiyar ministan muhalli.

XS
SM
MD
LG