Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Neman Hanyar Ceto Dalibai Ba Tare Da Amfani Da Karfin Soja Ba-Masari


Jama'a sun taru a makarantar da aka sace dalibai.
Jama'a sun taru a makarantar da aka sace dalibai.

Gwamnan Jihar Katsina Aninu Bello Masari ya bayyana cewa gwamnati na kokarin ganin an ceto ‘yan makarantar da mahara su ka yi garkuwa da su ba tare da musayar wuta ba domin kare lafiyarsu.

A cikin hirar shi da Sashen Hausa, gwamna Masari yace bayanan sirri da jami’an tsaro suka samu na nuni da cewa, wadansu yaran suna makwabciya jihar Zamfara inda aka sa su ayyuka sai dai yace kawo yanzu ba za a iya bada cikakken bayani kan yanayin da yaran suke ciki ko kuma matakan da ake dauka na ceto su sabili da dalilai na tsaro.

Makarantar sakandaren Kankara da aka sace dalibai
Makarantar sakandaren Kankara da aka sace dalibai

Gwamna Masari ya bayyana cewa gwamnati ta kafa cibiyar samar da bayanai da suka samar da lambobin za da za a iya aika sakonni ko kuma bayar da bayanai da zasu taimaka wajen ceto daliban. Cibiyar zata kuma rika samar da bayanai ga manema labarai kan halin da ake ciki.

yadda-daya-daga-cikin-daliban-da-aka-sace-a-katsina-ya-kubuta

sojojin-najeriya-sun-gano-inda-wadanda-suka-sace-dalibai-a-katsina-suke

iyaye-a-katsina-sun-yi-zanga-zangar-neman-a-ceto-ya-yansu

Ya kuma kara kira ga iyaye su ci gaba da hakuri da addu’oi yayinda gwamnati ke iyakar kokarin ceto ‘yan makarantar. Ya kuma yi alkawarin daukar dukan matakan da suka kamata na tabbata cewa haka bata sake faruwa a makarantu ko kuma wuraren tarukan jama’a da mata da kananan yara su ke zuwa ba.

Makarantar da aka sace dalibai
Makarantar da aka sace dalibai

Tun farko gwamnan Masari ya kai ziyarar gani da ido a makarantar da aka sace daliban kashe garin aukuwar lamarin, tare da bada umarnin rufe dukannin makarantun kwana a jihar domin gudun sake afkuwar lamarin, yayinda kuma ya yi tattaki domin yi wa shugaba Muhammadu Buhari bayani kan halin da ake ciki.

Tuni kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin kai harin sai dai kawo yanzu, gwamnatin tarayya bata maida martani dangane da ikirarin Abubakar Shekau shugaban kungiyar na kai harin ba.

Saurari hirar da Sani Shu’aibu Malumfashi ya yi da gwamna Masari.

Hira da gwamna Aminu Bello Masari:2:58"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00


Karin bayani akan: Boko Haram, sojoji, Masari, da jihar Katsina.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG