Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihar Katsina Ta Bada Umurnin Rufe Makarantun Kwana Bayan Sace Wasu Dalibai


KATSINA: Gwamnan Katsina Bello Masari

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ne ya bada umurnin a rufe dukkan makarantun kwana na jihar, biyo bayan sace wasu daliban makarantar sakandaren a garin Kankara da ke jihar.

A lokacin da ya kai ziyara makarantar ranar Asabar 12 ga watan Disamba tare da tawagarsa, inda ya gana da iyaye, malamai da sauran masu ruwa da tsaki na makarantar, gwamnan bai boye bakin cikinsa ba, ya kuma yi kira ga jama’a da su yi hakuri, tare da jaddada cewa gwamnati za ta yi duk abinda ya dace don tabbatar da an sako sauran daliban da aka sace.

Ranar Juma'a 11 ga watan Disamba, bayan sallar Isha ne dai ‘yan bindiga su ka kutsa makarantar sakadaren ta kimiyya a garin Kankara. Mai gadin makarantar ya shaida wa Muryar Amurka cewa wajen karfe 10:30 na dare su ka ji harbe-harben bindiga a bakin kofar shiga makarantar, sannan wasu ‘yan bindiga su ka haura ta katanga su ka shiga cikin makarantar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina SP Gambo Isah, ya tabbatar da aukuwar lamarin, ko da yake ya ce 'yan bindigar sun fuskanci tirjiya daga wasu ‘yan sanda da ke tsaron makaranatar bayan da su ka yi musayar wuta da su.

SP Gambo ya kuma ce an harbi daya daga cikin ‘yan sandan, amma ya na asibiti ana jinyarsa, ya kara da cewa ya zuwa safiyar ranar Asabar an samu nasarar ceto dalibai kusan 200, amma har yanzu ana ci gaba da bincike tare da hadin gwiwar hukumomin makarantar da jami’an tsaro domin tantance da gano daliban da aka sace.

Gwamnatin Najeriya ta yi Allah wadai da harin da ‘yan bindigar su ka kai a makarantar sakadaren tare da jajanta wa iyayen daliban, da shugabannin makarantar, da wadanda suka jikkata, sakon da mai magana da yawun fadar gwamnatin Najeriya Malam Garba Shehu ya rubuta kenan a shafinsa na Twitter. Bayan haka Shugaba Buhari ya yi alkawarin ci gaba da tallafa wa 'yan sanda da sojoji masu gwagwarmaya da 'yan ta'adda da 'yan bindiga.

Saurari cikakken rahoton Sani Shuaibu Malumfashi:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00

Karin bayani akan: Bello Masari, sojoji, da jihar Katsina.

XS
SM
MD
LG